1 Nuwamba 2020 - 14:31
Iran Ta Sanar Da Sake Daukar Wasu Sabbin Matakai Don Daƙile Cutar Korona Da Ke Yaɗuwa A Kasar

Shugaban ƙasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya sanar da cewa gwamnati za ta ɗau wasu sabbin matakai ciki kuwa har da taƙaita zirga-zirgar jama’a a yankuna da daman a ƙasar a ƙoƙarin da gwamnatin take yi na daƙile ci gaba da yaɗuwar cutar nan ta Coronavirus da ta sake kunno kai a ƙasar.

ABNA24 : Shugaban ya sanar da hakan ne a wani jawabi da yayi ta gidan talabijin na ƙasar bayan zaman da kwamitin kula da cutar koronan ta ƙasar Iran yayi a yau ɗin nan Asabar inda ya ce matakan killacewar za su shafi larduna 25 cikin 31 na ƙasar ciki kuwa har da gundumomi 46.

Sanarwar dai ta ce za a fara aiwatar da wannan killacewa da tsagaita zirga-zirgan ne daga ranar Laraba mai zuwa inda za a rufe wajajen taron jama’a irin su gidajen sinima, wajen shan shayi da kayayyakin zaƙi, wajajen motsa jiki da wajajen ninƙaya har na tsawon kwanaki 10. Kamar yadda kuma za a dakatar da duk wasu tarurruka na jama’a sannan haka nan makarantu ma za a koma karatu ta hanyar intanet.

A bisa sanarwar da kakakin ma’aikatar lafiya ta Iran ɗin, Sima Sadat Lari, ta yi a yau din nan Asabar ta ce mutane 386 ne suka rasa rayukansu a yau ɗin sakamakon cutar ta Korona, inda wasu sama da 7,820 kuma suka kamu da cutar.

Cikin ‘yan kwanakin nan dai adadin masu kamuwa da cutar da kuma waɗanda suke rasa rayukansu a ƙasar Iran yana daɗa ƙaruwa lamarin da ya sanya gwamnatin ɗaukar wasu matakai don daƙile yaɗuwar cutar.

342/